Lokuta da dama mu kan tafi neman mafita ga duk wani abu ko wata tawaya da ta yi mana kaka-gida.
Kuma ba na tunanin hakan akwai laifi a ciki, sai dai in mutum ya kauce wa hanya yayin neman magance tawayar ko damuwar.
Lamarin farin jini ba karamin gagarumin lamari ba ne, domin ya kan haifar da tarin matsaltsalu da damuwoyi wadanda ba sa da iyaka.
***
Allah (S.W.T) shi ne ya haliccemu, kuma cikin hikimarsa da iyawarsa sai ya yi mu gamu nan duk mutane muke amma kuma kowa daban ya ke da ‘dan ‘uwansa.
A bangaren haibarmu, da surar halittarmu ma sai ya bambanta mu. Bugu-da-kari a bangaren farin jini ko bakin jininmu ma sai ya kara bambanta mu, wasu su ka fi wasu, wasu kuma ba su kai wasu ba.
Tabbas, shi din gagarabadau ne!
***
Farin Jini
“Shi ne mutane su so ko kaunaci wani mutum ko abu.”
In aka ce mutum ana nufin mutane su ji suna kaunar wane ko wance. Sannan in aka ce abu ana nufin mutane su ji suna son wani kaya kowanne iri ne, ko su ji suna son zuwa wani gari, kasuwa, shago da sauransu.
Shi farin jinin kasuwa ko na mutum rankatakab dinsa ba ya faruwa sai da wani dalili.
In farin jinin mutum ne, to za ka samu mutumin da wasu nagartoci tattare da shi. Daga cikin nagartocin za a samu ko kyakkyawa ne, mai kyaun hali, mai iya mu’amala da sauransu.
Shi kuma farin jinin kasuwa shi ne nau’in farin jini da mutane za su ji kawai suna son zuwa kasuwa kaza, shagon wane da wane da wance domin su sayi kaza.
Ko kuma su ce wurin wane wanda ke kasa kaya iri kaza su saya.
Bugu-da-kari, shi ma ba ya samuwa sai in har mai gudanar da wannan wuri yana da wasu nagartocin kasuwa kamar su faran-faran da jama’a, sauki ko rahama, fadar gaskiya da kawo kaya mai kyau.
***
Maganin Farin Jini
In har na ce muku babu wani maganin farin jini [walau na rubutu, addu’a, gargajiya da sauransu] to gaskiya zan iya cewa na yi muku karya.
Akwai lakanunnuka masu tarin yawa na farin jini wadanda daga cikin Al-Qur’ani aka zakulo su.
Wasu daga cikinsu rubuta ma za a rinka yi a allo kana sha, wasu kuma kawai addu’a ce za ka rike kana karantawa.
In kuma ka dauke wannan, sai kuma maganin farin jini na gargajiya wanda shi kuma hade-haden magunguna ne wanda masu maganin gargajiya ke hadawa, su kan ce yana maganin farin jini.
Amma dai, a iyakar karamin sani na, wanda ya fi aiki kwarai da gaske bai wuce wanda ake rubutawa a sha ba, sai kuma wanda za a baka addu’a ka rinka yi kullum domin farin jini ya karu.
Haka kuma duk da haka, farin jini bai samuwa sai in har mutum yana da wadansu nagartoci, ko kasuwarsa na da wadannan nagartoci.
Ko ma dai menene, kada ku bari wani ya burma ku, ya baku ganyayyaki ku yi ta bunka kuma babu sauyi.
Addu’ar Farin Jini
Akwai tarin addu’o’i da shawarwari wanda Manzon Allah (S.A.W) ya bayar wadanda mai bukatar farin jininsa da kwarjininsa su karu a idon mutane ya juri yinsu.
Wasu daga ciki da zan kawo, sun zo ne a cikin Al-Kur’ani, wasu daga Manzo, wasu kuwa daga mutane masu fikirar zance.
Ya kamata mu yi sani cewa, ba a makara da shuka alkhairi, duk wanda ya juri kyauta, to mutane za su so shi.
Wadannan abubuwan guda biyu zuwa uku wato:
- Saukakawa / rahama
- Kyakkyawar mu’amala
- Da kyauta
Suna matukar sa wa a so mutum domin Manzon Allah (S.A.W.) da kansa a wani ingantaccen hadisi ya ce:
“Ku yi kyauta za a so ku.”
Bugu-da-kari a cikin wani sahihin hadisin ma ya ce;
“Hannun da yake bayar wa shine a saman hannun da yake karba a koda yaushe.”
Sannan shi kansa Malam Bature ma cewa ya yi; “Givers never lack” ma’ana mai bayarwa ba ya rasawa.
In mu ka yi duba na tsanaki, na hankali game da abubuwan da mu ka karanta, sai mu fahimci cewa ashe kyauta rahama ce kuma ta kan sa a so mutum.
Haka kuma kyakkyawar mu’amala kan sa mutane su so yin mu’amala da mai ita. Sannan duk wanda ya ke saukakawa mutane a kan kasuwarsa, to, sun fi son zuwa siyayya wannan kasuwar tasa.
A bangaren Addu’o’i rubutattu wadanda ake yin laziminsu, ko sururorin Al-Kur’ani wanda ake rubutawa a sha, su ma wasu nan mun kawo muku domin ku amfana.
Addu’a da Lakanin Farin Jini
Wannan zan baku shi ne daga cikin irin lakanunnukan da na samu lokacin da nake Aljamiranci.
Malamin da ya bani wannan addu’a ya ce in dai mutum yana son ya yi farin jinin jama’a ko na kasuwa to ya rungumi wannan addu’ar.
Aya ta 9 a cikin surar Al-Imran. Ga ta nan kamar haka:
رَبَّنَا إِنَّكَ جَامِعُ النَّاسِ لِيَوْمٍ لَّا رَيْبَ فِيهِ
Transliteration dinta kuma:
Rabbana innaka jamiAAu annasi liyawmin la rayba feehi
Yadda Ake Amfani Ayar
Ka samu almajiri sai ba bashi ayar babu wasali, ya rinka yi maka rubutu yana kawo maka kana wankewa kana sha da bismilla.
Ko kuma ka rinka yin lazimi da ita, kana yawan maimaitata da carbi. Da yardar Allah in dai matsalarka ta jama’a ce, da farin jininsu, to, Allah zai kawo maka su.
Addu’ar Farin Jini daga Sheikh Fantami
A cikin wani post da dan Jarida wakilin Freedom Radio ya yi a shafinsu na yanar gizo, ya kawo wani nau’in maganin farin jini wanda fitaccen Malamin Islamar nan, Dakta Isa Ali Pantami ya bayar.
A shafin Twitter (X) wani mutum ya roki Malam inda ya ce:
“Malam a taimaka mana da maganin farin jini muma.”
Ba tare da wani bata lokaci ba sai Malam ya bashi amsa da cewa:
“Kwatanta bin dokokin Allah da addu’ar iyaye.”
Sharhi
Ba wai don mun fi Malam sani ba ko fahimta, amma abin da Malam ke nufi shi ne: duk wanda ya kwatanta bin dokokin Allah sau da kafa kuma ya bi iyayensa har su ke yi masa addu’a, to lallai zai samu farin jini.
Addu’ar Farin Jini a Musulunci
Manzon Allah ya bayar da wani sahihin maganin farin jini wanda ake yinsa ta hanyar amfani da daya daga cikin kyawawan tsarkakan sunayen Allah 99.
Kamar yadda aka wallafa a shafin Amsoshi, an ce a wani ingantaccen hadisi Manzon Allah (S.A.W.) ya ce, duk mutumin da ya kira sunan Allah “Ya Ar-rahamar rahimeen” sau uku, to wani Mala’ika zai tsaya kusa da shi yace masa “Ga Arahmanur rahimeena nan ya juyo gareka.” N
Nan take duk abin da mutum ya roka Allah zai amsa masa.
Sharhi
Wannan dama ce ga mutumin da ke bukatar hanyar da zai roki Allah farin jini kowanne iri ne, walau farin jinin samari, ‘yammata, kasuwa da sauransu.
Duk wani musulmin kwarai to kada ya yi sake da wannan damar, domin hanya ce ta samun kusaci da mahalicci.
Maganin Farin Jini da Suratul Yusuf
Hakikanin gaskiya wannan zai iya kasancewa Lakani ne, domin wani bawan Allah mai suna Alaramma Aliyu ne ya wallafa shi shekaru hudu da suka gabata wato 2020.
Ya ce duk wanda ke son yin farin jini ko kwarjini to, ya rubuta Suratul Yusuf baki dayanta a kan Madubi [madubi fa wanda ku ka sani] sai a wanke ta.
Kai in ma madubin bashi da girma sosai, to za a iya rubutawa kadan-kadan ana wankewa.
Yayin da aka zo kan Aya ta 31 sai a maimaita rubutata daga wannan wajen “Falamma ra’ainahu akbarnahu” har zuwa karshen ayar.”, gashi nan mun kawo shi a kasa.
فَلَمَّا رَأَيْنَهُۥٓ أَكْبَرْنَهُۥ وَقَطَّعْنَ أَيْدِيَهُنَّ وَقُلْنَ حَـٰشَ لِلَّهِ مَا هَـٰذَا بَشَرًا إِنْهَـٰذَآ إِلَّا مَلَكٌۭ كَرِيمٌۭ
Bayan an yi nasarar rubuce surar a kan allon, an wanke rubutun. To, abu na gaba shi ne sai a samu ‘Garin Tumfafiya’ a zuba shi a cikin ruwan sannan sai a sha.
Da yardar Allah in dai za a juri yin haka, to za a samu farin jini da kwarjini kwarai da gaske.
Kada mu manta
Komai da mu ka sani da yardar Allah ya ke aiki, Ba wai wayo ko wani abu na mutum ne ke sanyawa ya yi ba. Sannan kada a sha rubutun ba tare da yin bismillah ba.
Kammalawa
Yin farin jini ko bakin jini akwai wadanda ya kan zo musu ne daga Ubangiji, amma in dai kana kyauta, za ka yi farin jini, in kuma kana rahama akan sa’anarka, to sana’arka za ta yi farin jini.
Haka kuma, iya mua’amal da mutane ma kan sa mutum ya yi farin jini.
Da-haka-da-haka za mu rufe jawabinmu na yau, zuwa wani lokacin kuma za mu fidda lokaci domin sabuntawa da kara wasu abubuwan a ciki.