Ciwon Basir da Alamominsa da Magani Basir Kowane Iri

Advertisement
Magungunan Gargajiya
Image by Seksak Kerdkanno | Pixabay

Har yau har gobe, babu wani sahihin magani wadda ke dakile cutar ciwon basir baki dayanta.

Domin in dai gari zai waye ka tashi daga barci, ka fito, ka samu wuri ka zauna, ka zazzaga ka dawo, ka kara zama, ko ka yini kana zaune, to, ba ka da ranar rabuwa da basir baki dayansa.

Sai dai mu ce za ka samu sauki, za ka kuma waraka daga wannan lalura ta basir na ‘dan lokaci, ko dogon lokaci, amma dai ba a rabuwa da basir muddin mutum zai na zama. Shi kuwa zama wajibi ne ga ‘Dan Adam.

Darasinmu na yau ya kunshi cikakken bayani akan basir, musabbabinsa, alamominsa (symptons), matakansa a likitance (stages), da magungunansa iri-iri kama daga kan na Malam Bature har zuwa kan namu na gargajiya.

Ku yi sani cewa: Babu wani tabbas (guarantee) akan maganin basir na gargajiya da zan kawo muku a cikin darasin nan, sai kun gwada tukunna. Wanda Allah ya yaye wa sai ya yi masa godiya. Wanda kuma bai samu nasara ba sai ya gwada wani.

Game da maganin bature: Magunguna ne wadanda sai da aka yi bincike a kansu, hukumomi su ka yarje da su tukunna kafin a sake su ga dukkanin al’umma su amfana. Amma duk da haka, kada ku sha wani magani har sai kun tuntubi likitanku.

Bugu-da-kari, duk wani abu da za ku ci karo da shi, to ba gaba-gadi mu ka wallafa shi ba, sai da mu ka yi binciken kwakwaf akansa tukunna.

Ciwon Basir

Duk wata cuta da ku ka sani akwai musabbabinta, don haka ita ma lalurar basir ba a barta a baya ba, da na ta sanadin.

Ba fa komai ne basir ba face rashin lafiyar kananun jijiyoyin da ke bango-da-bangon dubura wadanda aikinsu shi ne su samar da jini ga dubura don hana ta bushewa ko lalacewa.

Haka kuma suna daukar jini daga duburar mutum su mayarshi cikinsa, daga nan zuwa zuciyarsa.

Yayin da aka samu sabani wadannan jijiyoyin su ka cika da jini sakamakon yawan zama [wato aka takure su ba sa iya samun damar yawatar da jinin nan] sai jinin da ke cikinsu madadin ya yawata jiki sai ya cika jijiyoyin, daga nan sai ya haifar da kumburi [ko kololo].

Shi wannan kumburi in aka dauki lokaci shi ne za ku ga ya fito wa mutum a wajen duburarsu, ko a shatin duwawunsa inda ya ke zama.

Amma kafin ya fito ya yi girma, ‘dan karami ne zai fito sai a rinka jin yana zugi in an zauna a kansa, a haka zai cigaba da girma muddin ba a dauki matakan da suka dace a kansa ba.

Bugu-da-kari, duk ranar da jinin nan ya taru ya daskare a cikin kananun jijiyoyin duburar nan sai a ga basir din ya yi karfi kwarai da gaske har ya matsa wa mai shi da shegen ciwo wanda ke sa mutum kasa zama a kasa, ko kan benci, ko kujera marar katifa [kai ko da katifa sai da dabaru].

Babu shakka ina da tabbacin kun fahimci abin da ake nufi da ciwon basir da abin da ke haifar da shi.

Bari mu ga me ke kawo shi wannan ciwo na basir kuma.

Karin abin da ke kawo Basir

Wani likitan ‘dan jihar Kano, Dakta Ibrahim Y. Yusuf ya bayyana galibin abubuwan da ke kawo cutar basir a cikin wani bayani da yayi game da ciwon basir a shafinsa na Facebook.

Ga abin da yace:

  • Yawan zama wuri daya na tsawon lokaci: Musamman ga teloli, direbobi, ma’aikata office da dalibai ‘yan makaranta
  • Attini (constipation): Shi ma jawo basir domin ya kan sa a yi bayan gida mai tauri wadda ke fitowa da jini ko babu.
  • Juna biyu: Sakamakon nauyin da cikin ya yi, in mace ta je tsugunno hakan na sa jijiyoyin duburarta su matse wadda hakan ke haifar da basir. Kamar yadda ya bayyana mafi akasarin mata sai sun samun juna biyu suke kamuwa da basir.
  • Kiba (over weight): Kiba na jawo basir saboda in mutum mai kiba ya je bayi yana tsugunnawa nauyinsa zai sauka mararsa wanda hakan zai sa dubura ta yi matsi.
  • Yawan gudawa (zawo): Yawan zawo shi ma na sa cutar basir, amma hakan ya fi faruwa ga wadanda ke da cuttutuka irin na hanji (IRBS) ko HIV kuma ba sa shan magani.
  • Gaggawa wurin yin kashi: Akwai masu halayyar son lallai sai sun kasaye abin da ke cikinsu saboda suna fama da atini, sakamakon yunkurin da suke yi da karfi hakan zai iya haifar musu da basir
  • Tebar kugu: Tara teba a kugu (duwawu) ko wajen mara (wato tumbi) shi ma na jawo basir. Kuma ba ga iya maza ya tsaya ba, har da mata
  • Nakuda: Ita ma tana iya haifar da basir kuma hakan na faruwa ne mafi akasarin lokuta in mace ta haihu da kanta
  • Jima’i ta dubura: Bayan tarin cututtukan da hakan ke haifarwa, tarawa da mace ko namiji ta dubura na jawo basir.

 

Kada ka yi tunanin saboda mun jero wadannan abubuwan da Dakta ya fada hakan na nufin iya su kenan, a’a, akwai karin wasu abubuwan da ke kawo ciwon basir.

Amma dai mu za mu dakata a nan, sai mu gangara kan alamomin ciwon domin kara fadada jawabin namu.

Alamomin Basir

Yana da kyau in ba ka da lafiya ka san ba ka da lafiya. Kuma in har basir ne matsalar taka to ka san alamominsa domin sanar da wadanda ba su sani ba.

Daga cikin alamomin basir akwai:

  1. Dubura ta kumbura
  2. Dubura ta na fitar da jini (haka kumu ba tare da an ji zafi ba)
  3. Ciwon jiki ko rashin sakewarsa
  4. Bacin rai ko dubura ta rinka kaikayi
  5. Ka ji wani abu ya fito maka yana ma kaikayi a katarya
  6. Ka ga curi ko dunkulen jini na fita duburarka

Wadannan kadan kenan daga cikin alamomin da ke nuni da cewa kana dauke da basir.

A karshe, ku fada bincike don ba lallai iya wadannan ne alamomin ciwon basir ba.

Nau’ikan basir (mai tsiro)

Duk da basir na da matakansa (stages) a likitance, amma ba za mu fara da yi muku bayani a kansu ba.

Za mu fara ne da ire-iren basir dan kanoma wato mai tsiro wanda a turance ake kiransa hemarrhoids, da ma shi muke magana a kai.

Basir (mai tsiro) ya kasu gida biyu, daga ciki akwai:

  1. Basir din ciki (internal hemarrhoids): Nau’i ne na basir wanda ke fitowa a can cikin duburar mutum. Ba za ku taba ganinsa a waje ba.
  2. Basir din waje (external hemarrhoids): Nau’in basir ne wanda mu ka saba gani wanda ya ke yin tsiro ya turo kai waje, irin basir din da ke hana mutum zama. Kuma ana ganinsa ta madubi ko a taba.

Yanzu kuma za mu shiga cikin matan cutar ciwon basir (stages) a likitance.

Dakta Ibrahim Y. Yusuf ya yi bayyana cewa stages wato matakai na lalurar basir sun kasu gida hudu, sannan muddin aka bari basir din nan ya faro daga matakin farko (stage 1) ba tare da an dauki mataki ba har ya kai mataki na hudu (stage 4), to da matsala.

Ga dai matakan nan mun jero;

  • Stage 1: A wannan mataki mutum zai fara jin zafi ne a duburarsa, sannan in ya yi bayan gida sai ya ga jini da majina sun biyo baya. Bugu-da-kari, ko da ya shafo duburarsa ba zai ji alamun tsiron basir ba.
  • Stage 2: A wannan matakin duk lokacin da mutum ya kammala bayi in ya sa hannu zai ji jijiyar basir din ta zazzago yadda zai iya taba ta. Amma bayan ya wanke bayin da kanta jijiyar zai ji ta koma.
  • Stage 3: Shi ne matakin da mutum na kammala bayi zai ji ta zazzago, sannan ko ya wanke ba za ta koma ba dole sai ya sa yatsa ya mayar da ita [duburar]. Kuma yana mayarwa zai ji ta koma.
  • Stage 4: A matakin nan na karshe shi ne in mutum ya yi tsugunno zai ji bayansa ya zazzago, yayin da ya yi kokarin mayarwa kuma ya sha azaba. Kuma ko ya mayar, haka kurum sai ya ji ya kara zazzagowa.

Yayin da lalurar nan ta hemorrhoids (basir) ta kai wannan mataki na hudu, to an riga da an gama samun matsala domin dole sai mutum ya je ya ga likita.

Baya ga haka wajibi ya hada da neman maganin gargajiya wanda ke warkar da irin wannan nau’in basir din, in kuma aiki za a yi masa sai ya tuntubi masana lafiya.

Bugu-da-kari, ita fiyar baya basir ke haifar da ita, sannan da zarar ka ga baya ya fara fito ma, to hakan na nuni da cewa basir dinka ya je matakin karshe.

In ba zan manta ba, kanena wanda ke bi na, yana ‘dan karaminsa ya kama fitar baya, a haka zai yi bayi, a wanke masa sannan a mayar ta.

Amma da aka dage da magani tun kafin ya kammala wayo abin ya zama tarihi ya samu lafiya saboda haka kai ma da basir ke damunka za ka samu lafiya.

Hanyoyin Rigakafin Basir

A ko ma menene, an ce rigakafi ya fi magani. Ni kaina na yarda da hakan, wannan shi yasa na yi bincike na musamman domin baku wasu shawarwari da matakan da ake bi wurin kare kai daga kamuwa da cutar nan.

  1. Ku na yawan cin kayan marmari
  2. Ku na shan ruwa sosai
  3. Ku guji matsawa dole sai kun kasaye abinda ke cikinku domin hakan na takura duburarku
  4. Ku na motsa jiki akai-akai
  5. Kada ku rinka zama a wuri daya na dogon lokaci.
  6. Ku kuma rinka amfani da kujera mai taushi in za ku zauna.

Wadannan su ne wasu daga cikin matakan da ake bi wurin yin rigakafin basir.

Kuma abin da zan fi mayar da hankali na akansa shi ne; ku rinka yawan motsa jiki, cin abinci mai kyau, rage zaman wuri daya na dogon lokaci dss.

Yanzu, zan kawo muku magungunan basir na bature.

Maganin Basir na Bature

Magana ta gaskiya kamar yadda na bincika babu wani takamaiman maganin basir a likitance wanda kai tsaye ya ke magance cutar, sai dai rage radadinsa.

Kuma wadannan magunguna wasu daga cikinsu kamar yadda Dakta ma ya yi bayani ana siyar da su a kyamis-kyamis.

Sai dai: Ni ba zan shawarceku da ku yi amfani da su kai tsaye ba ba tare da tuntubar jami’an lafiya ba.

Daga cikinsu akwai:

  • Topical anesthetic
  • Hemorrhoidal cream
  • Anosul dss.

Duk inda ku ka bincika a asibitoci ko wuraren sayar da magunguna za ku same su, amma kada ku sha har sai kun tuntubi likitanku.

Hanyoyin Magance Basir ba Tare da Magani ba

Wannan zai kasance wani abin mamaki ba, domin in har akwai rigakafin da ake yi wurin dakile kamuwa da cutar basir, to hakan na nufin akwai hanyoyin da za a iya bi wurin magance shi ba tare da an sha magani ba.

Haka kuma in mutum ya dage da bin wadannan hanyoyi to zai tsinci kansa cikin mutane da ba sa shan wahala yayin bayan gida.

Kun san makasudin cutar basir fa zama wuri daya ne da dattin ciki.

1. Motsa Jiki

Da kai ko ke mabibiyyar rubututtuka na ne, da za ka fahimci cewa yana daga cikin dabi’ata shawartar mutane su na motsa jiki.

Yawan motsa jiki na taimakawa wurin kone duk wadansu kananun cuttuka da ke jikin ‘dan Adam.

Yana kara wa mai yi kuzari, yana taimakawa wurin tsinka jini ya zaga ko ina, inda daskararren jini ya ke (basira jijiyar dubura) zai tsinke.

2. Cin Abinci Mai Gina Jiki

Wani abu da wasu daga cikinmu ba su sani ba shi ne; shi fa cin abinci mai gina jiki tasiri da yake da shi ga ginuwar jikinmu da lafiyarsa ba kadan ba ne.

Sannan in kana cin abinci mai gina jiki zai taimaka wurin magance basir din da ke damunka.

Bugu-da-kari cin irin nau’ikan abincin da ke gina jiki na taimakawa wurin rage wahalar yin bayi.

Daga cikin irin abinci mai gina jiki akwai irin su ganyayyaki, da kayan marmari, kayan hatsi da sauransu.

Kuma irin su lemon juice da ku ke sha ba wata lafiya ke kara muku ba, gwara ma ku sha lemon bawo domin inganta lafiyarku.

Sanna ku rage cin abinci mai maiko da cin jan nama domin suna kawo basir.

3. Yawan Yin Wanka da Ruwan Dumi

Yana daga al’adar mutanen birane yin wanda da ruwan dumi, musamman ma wadanda ke fita kasuwa.

To, in har kasance kana yinsa. Zan so jaddada maka cewa ka ci gaba da yi abinka domin yana da tasiri ga lafiyarka.

Mutanenmu na kauye ku ma ku sarki wannan ta’ada domin tana taimakawa wurin magance lalurar basir ko kamuwa da ita.

Kananun cututtuka kamar su kaikayin jiki, da ciwon jiki duk ba za su uzzura maka ba.

4. Shan Ruwa Mai Kyau

Yanzu wani fa in har ka tambayeshi wanne irin ruwa ne ruwa mai kyau?

Kai tsaye fa pure water zai ce maka ko? To, magana ta gaskiya ruwa mafi kyau shi ne tap water (wato ruwan fanfo) sai ruwan roba wanda kamfanunuwa suke samarwa, sai kuma na rijiyoyi.

Ruwan famfo ba ya zuwa gareku sai an tsabtace shi da alimun daga matata, yayin da na roba ma haka.

Shi ma pure water haka, amma bai kai na famfo ba saboda mafi akasari a tsoffin rijiyoyi suke jawo ruwan da suke amfani da shi wurin yin pure water sannan ba kowanne ke da dadi ba.

Shi shan ruwa mai kyau na da matukar amfani garemu, domin ana wanken hanjin ciki da taimakawa wurin nika abinci.

In har da gaske kana son yin bankwana da lalurar basir, to, sai ka juri shan ruwa mai kyau.

5. Yin Tu’ammali da Vitamin C

Ko da na ce ku mu’amalanci Vitamin C, ba fa ina nufin ku samu kwayarsa kuna sha ba ne.

A’a, abinda nake nufi shi ne; ku na yin duk wani nau’i na abinci mai dauke da sinadarin Vitamin C.

Su irin wadannan nau’ikan abinci sun hadar da lemon tsami, tuffa, lemon bawo, kankana, kabeji, lemon grass, abarba, ayaba, tumatir, na’a-na’a, lettuce da sauransu.

Fa’idar mu’amalantar irin wannan cima ita ce; shi sindarin Vitamin C na kara wa jijiyoyin jikin ‘dan Adam lafiya sannan yana yin namijin taimako wurin dakile cutar basir.

***

Sai yanzu mu ka zo gabar da za mu kawo muku magungunan basir iri-iri domin amfaninku.

Amma ku yi sani cewa babu wani maganin basir wanda ya ke na Musulunci, kowanne na gargajiya ne.

Kada ku bari wasu su rinka yin amfani da addini suna yi muku wasa da hankali har ma da raina muku shi.

***

Maganin Basir Mai Tsiro

Kai tsaye a iya nan za mu kawo muku nau’ikan magunguna kamar guda hudu da yadda za ku hada su amma a saukakakken bayani.

Magance Basir Mai Tsiro da Kitsen Damo

Ku je wurin mafarauta ko kasuwar sassan namun daji ku samu kitsen damo amma mai kyau.

Bayan kun samu, sai a narka rinka shafawa a wajen da tsiron basir din ya ke. Da yardar Allah za a samu sauki a dace.

Mun samo wannan hadin magani ne daga Taskar Murtala Kawo.

Magance Basir Mai Tsiro da Mayuka Biyu

Ku samu castor oil, sai ku samo man na’a-na’a ku gauraya su ku rinka shafawa a wurin da basir mai tsiron ya ke.

Sannan ku rinka shan mayukan biyu cokali guda kullum. Da yardar Allah za a samu sauki a dace.

Mun samo wannan hadin magani ne daga Taskar Murtala Kawo.

Magance Basir Mai Tsiro da Danyen Sassaken Dinya

Ku samu sassaken dinya ku tafasa shi. Sai ku samu farin ruwa ku ‘dan sirka shi yadda za ku iya zama cikinsa.

Sai ku zuba ruwan a bahon wanka, ku zauna a ciki na kamar mintuna talatin.

Ku yi haka kullum kamar na tsawon sati biyu. In Allah ya yarda sai ku ga an dace.

Magance Basir Mai Tsiro da Wannan

Da fari dai ku samu man tafarnuwa, habbatus sauda da na zaitun. Bayan kun tanadi wadannan mayuka sai ku samo auduka ku aje gefe.

Abu na gaba sai ku hade wadannan magunguna a cikin kwalba ku gauraya su sosai.

Duk lokacin da za ku kwanta, sai ku yagi adugur nan ku lakaci maganin da ita, sai ku shafa a daidai inda basir din ya tsir muku sannan ku kwanta.

Insha Allahu za a samu sauki, amma fa a ankare, wannan hadin yana da zafi.

Magance Basir Mai Tsiro da Wannan II

Ku samu garin hulba, bagaruwa, da na sassaken dinya.

Sai ku hade su wuri guda, ku na diba kuna dafawa kuna zama a cikin ruwan zafin.

Sai dai kada ku na zama cikin ruwan da kunansa, ku rinka zama da duminsa.

Magance Basir Mai Tsiro da Wannan III

Ku nemi garin qirfa kamar cokali 3, sai ku dafa shi da ruwa kofi guda. Sannan sai ku saka zuma a ciki ku na sha.

Bayan haka sai ku tafasa sassaken dinya, in zafinsa ya yi ramai-ramai sai ku zuna a cikinsa. Kullum ku yi haka sau biyu.

Da yardar Allah za ku dace.

Magance Basir Mai Tsiro da Wannan IV

Ka samu garin bagaruwa, sai ‘ya’yan raidore da kumfar maliya.

Abu na gaba sai ka hade su wuri guda ka tafasa su. Sai ka sauke tukunyar ka kai daki, sai ka tsugunna tururin ya dinga shiga jikinka.

Idan ya huce sai ka juye ruwan ka kai bandaki ka zauna a ciki ko ka na kama ruwa dashi.

Maganin Basir Kowanne Iri

Domin dakile basir ko ma wanne iri ne da ke damunka sai ka samu garin habbatus sauda, garin citta, garin sassaken dinya da zuma kamar kofi guda.

Sai ku debi garin habbatus sauda cokali 3, sassaken dinya cokali 1, na citta ma cokali daya ku zuba a cikin zumarku ku gauraya.

Sai ku rinka sha cokali biyu safe, rana, da yamma. Kullum dai su uku.

Maganin Basir Kowanne Iri II

Kamar yadda mu ka samu jawabi daga sassa daban-daban, shi wannan nau’in na maganin basir yana yin maganin basir kowanne iri ne.

Ku samu lemon tsami 3, jan gauta 3, tsohuwar tsamiya 3, barkono guda 5, sai kuma sabulun sha wanda girmansa ya kusa na lemon tsami.

Kana tanadarsu, sai ka zuba a mazubi, ka jika su ka barsu su kwana tukunna.

Sai ka na tsiyayar kofi guda kullum kana sha, sannan ka na kara ruwa a cikinsa har sai ka ji ya yi salama.

To, daga nan sai ka sake sabon jiko. Haka za ka yi har sai ka ji basir din ya sake ka.

Maganin Basir Kowanne Iri III

Ku nemi sassaken itacen kadanya, da mangwaro, da dorawa, da sassaken madaci [amma fa ‘dan kadan ake bukatar madacin].

Sai ku hada su wuri guda ku wanke, sannan ku kawo jar kanwa ku zuba sannan ku tafasa.

Kullum ku sha sau uku, amma kowanne lokaci rabin kofi za ku na sha.

Maganin Basir na Mata

Kusan duk irin nau’ikan magungunan basir din da muka kawo a sama, mata da maza za su iya amfani da su.

Amma ku kara sani cewa babu wani tabbas da muke da shi akan wadannan magunguna suna aiki, amm kuma dole sai kun jarraba za ku samu wanda zai yi muku.

Ga mazan da basir ya sa su ka samu matsala a fannin al’aurarsu har hakan ke shafar rayuwar aurensu, to, sai gareku.

Ku samu saiwar sabara da saiwar tsada, sai ku nemo sassaken diniya (amma dai ta ‘dan fi yawa fiye da sauran saiwoyin).

Bayan kun tanadi wadannan abubuwa sai ku shanya su, su bushe sannan ku hade wuri guda ku dake su, ku tankade iya garin.

Sai ku na diban cokali daya na garin maganin kullum ku zuba a mafadi, ku kawo ruwa kofi daya ku zuba, sannan ku dafa.

Bayan ya dahu sai ku tace, in ya yi sanyi sai ku sha.

Mutum zai ci gaba da yin haka ne har na tsawon sati biyu.

In dai matsalar ta karfin gaba ce, za a samu canji da yardar Allah.

Maganin Basir Sadidan

Ga dukkan alamu mun kusa zuwa inda za mu dasa aya a cikin wannan zuzzurfan jawabi namu akan lalurar basir wato hemorrhoids.

Ina son sanar da ku cewa duk wadannan nau’ikan magungunan basir da ku ka ga mun kawo fiye da goma duk za ku iya gwada su.

Kuma duk wanda ya yi muku aiki, to shi ne sadidan din cikinsu.

Bisa wannan dalili, na ke cewa ku gwada wanda ku ka ga zai fi muku saukin hadawa.

Kammalawa

Duka-duka dai a nan mu ka kawo karsen wannan jawabi akan lalurar nan ta Basir.

Kuma a ciki mun kawo muku duk wani bayani da ku ke son sani game da lalurar basir.

Kana, mun kawo muku nau’ikan magungunan gargajiya, babu na musulunci, na bature da suke akwai.

Da fatan Allah ya saka mana da Alkhairi.

Reliable desk that post contents and upload subtitles at Filmovity. For broken link report, advert or anything email: info@filmovity.com.ng

Related Posts