Alamomin Shigar Ciki na Sati Daya, Sati Uku, da Watan Farko

Advertisement
People Supporting Each Other
Image by Mohamed Hassan | Pixabay

Abu ne mai muhimmanci kowacce mace ta san alamomin da ke nuna shigar ciki, sa’annan ta fahimta idan ta ji ko ta ga wadannan alamomi da ke nuna tana dauke da sabon ciki.

Kafin mu yi nisa, zan so ku yi sani cewa mun tattaro wasu daga cikin bayanan nan ne ta cikin jawabin da Dakta Ibrahim Y. Yusuf ya yi, yayin da wasu kuma ta mujallun lafiya na tattaro su.

Tun kafin ki je asibiti, a gwada ki, a tabbatar kina dauke da juna biyu ko akasin haka, to yana da kyau ki san ta yadda za ki gane kina dauke da cikin ta yadda za ki je da kwarin gwuiwarki.

Shin Mace za ta iya Gane tana da Cikin Kafin Zuwa Asibiti?

Kwarai za ta iya, amma kamar yadda Dakta ya bayyana, ya ce ba fa kowacce mace ce ta san cewa batan wata shi ne babban abin da ke kawo juna biyu ba.

Sannan kwayoyin cuttukan da ke shiga mahaifa su ma suna kan gaba wurin kawo batan wata ba [wato rashin ganin al’ada], ko kuma rikicewar lissafin wata.

Karin abubuwan da ke kawo rashin ganin jinin al’ada sun hadar da:

  1. Rashin zama wuri daya
  2. Shayarwa
  3. Rashin samun hutu [sakamakon yin wasanni ma su tsanani]
  4. Fama da ciwon damuwa ko yawanta
  5. Haka kuma a lokuta da dama shan magunguna barkatai walau na gida ko na asibiti, to, su ma suna iya haifar da batan wata.

Abubuwan nan 5 da na jero, su ne wadanda Dakta ya bayyana suna haifar da matsalar rashin ganin jinin al’ada.

Duk da bayan su kamar yadda mu ka bayyana a baya, shigar kwayoyin cuta cikin mahaifa da samun juna biyu su ma suna iya haifar da batan wata.

Yanzu kuma za mu gangara kan alamomin ciki tun daga satin farko, sati uku, wata daya har zuwa tsufan ciki.

Alamomin Ciki na Sati Daya

Yayin da ciki ya shiga, a sati farko mafi akasarin mata ba sa fuskantar ko ganin wata alama ta ciki ya shiga jikinsu.

Sai dai duk da haka wasu matan na iya ganin wasu alamomi da ke nuna shigar cikin da wuri kamar su:

  1. Zubar jini: Wani irin zubar jini ne da ke faruwa kwanani 10 zuwa 14 bayan daukar ciki. Kuma yana aukuwa ne bayan kwayar halittar manin [da za a halitta] ya manne da rufin mahaifa.
  2. Kumewar nono: Mace za ta ji nononta ya kumbura ko ya kume.
  3. Gajiya: Mace za ta ji gajiya fiye da yadda ta saba jinta.
  4. Sauyin yanayi: Mace za ta ji yanayinta na saurin sauyawa [ko dai tana yin saurin fushi dss].
  5. Kamshi: Ko kuma mace ta ji tana jin kamshi [ko ma wanne iri ne] fiye da yadda ta saba.

Duk macen da ta ji a satin farko tana fuskantar ko jin irin wadannan alamomi to yana da kyau ta je asibiti domin a yi mata gwajin ciki domin ta tabbatar da cewa tana da shi ko a’a.

Alamomin Cikin Sati Uku

Duk bayanin da ke cikin alamomin ciki a satin farko, su din ne dai a cikin alamomin ciki a sati na uku.

Abin da kawai ya bambantasu shi ne; a sati na uku mace ka iya jin alamomi kamar:

Sha’awar Abinci ko Kyamarsa

A sati uku da daukar ciki mace ka iya fuskantar kamuwa da sha’awar wasu nau’ikan abincin daban sannan kuma ta ji ta tsani ko kyami wasu nau’ikan.

Hakan na faruwa ne sakamakon sauyi da aka samo a hormones dinta.

Tashin Zuciya

Wasu matan na iya fara jin tashin zuciya ko kuma da sassafe su tashi da ciwo [na jiki dss] makwanni uku da daukar cikinsu. Kuma hakan ka iya faruwa a kowanne lokaci [da safe, maraice, yammaci ko dare].

Rashin Ganin Jinin Al’ada

Rashin ganin jinin al’ada ita ce alamar da aka fi sani da nuni da mace ta samu juna biyu. Duk macen da ke dauke da ciki wanda ya kai makwanni uku, to za ta iya ganin daukewar jinin al’ada.

Sai dai likitoci sun tabbatar da cewa ba fa kowanne daukewar jinin al’ada ne ke da alaka da daukar ciki ba. Matsaloli irin su damuwa, rashin lafiya ko kuma rage kibar jiki su ma ka iya haifar da daukewar jinin al’ada.

Yana da kyau a lura cewa ba duka mata ba ne za su fuskanci waɗannan alamomin ba, kuma wasu matan ba za su fuskanci wata alama ba kwata-kwata.

Alamu ko Alamomin Ciki a Watan Farko

Daga cikin irin alamomin da macen da ke dauke da cikin da ya kai kwanaki 30 za ta iya fuskanta akwai su batan wata sai kuma:

  1. Amai wasu lokutan da tashin zuciya da sassafe [kuma shi aman ko da ba a ci komai ba ya kan iya zuwa].
  2. Jin jiri (dizziness) yayin da aka zo mikewa ko saurin gajiya in an yi wani aiki
  3. Zubar da yawu
  4. Rashin son kamshi [na turaru, abinci dss]
  5. Zazzabi

Wadannan su ne alamomin da mace mai dauke da juna biyu da ya kai wata daya za ta iya fuskanta. Amma fa ba duk mata ke fuskantarsu ba duka ba, wasu ba ma sa fuskantarsu kwata-kwata.

Zuwa Gwajin Ciki

Yayin da mace ta je gwaji, ko kuma megidanta ya kai ta, to ana son a tabbatar da an fara yin gwajin ta hanyar auna fitsari.

Daga nan sai a yi hoton cikin [dalilin da yasa ya ke da amfani a yi hoton cikin saboda ta hoton ne za a iya tabbatarwa ta gangaran cikin a cikin mahaifa ya ke ko a wajenta ya ke].

Alamomin Cikin da ya Tsufa

Yayin da [ko a watannin da] cikin ya fara tsufa ya kai kamar watanni 3, to a kan iya ganin alamomi kamar su:

  1. Girman ciki
  2. Zarya ko yawan yin fishari [hakan na faruwa ne saboda abin da ke cikin cikin ya fara danne marar da ke aje fitsari]
  3. Yin ciwon baya
  4. Sai zafin katon zuci ko ciwon kirji ko kuma kwarnafi [wadda na faruwa ne sakamakon acid din cikin ciki na tasowa a kirji]
  5. Sai mace ta fara samun fitowar zane a fatar ciki da duhun fuska hadi da budewar hanci.
  6. Wasu matan kuma ke yin ciwon nonuwa ko su ji sun yi musu nauyi.

Yana da kyau mu yi sani cewa; ba fa kowacce mace ce ke fama da irin wadannan matsaloli ba yayin da su ke dakon ciki. Sai dai an yi ittifakin cewa rabin mata na gamuwa da akalla rabin wadannan alamomin.

Shawara Gare Ki

Ni a tawa shawarar, yana da kyau ki na ziyartar likita akai-akai in dai kin san kina da yaron ciki ko tsohon ciki domin a rinka duba miki lafiyarsa, yanayin kwanciyarsa da sauransu.

Allah kuma ya sauki duk mata masu ciki lafiya domin mata iyayenmu ne.

Reliable desk that post contents and upload subtitles at Filmovity. For broken link report, advert or anything email: info@filmovity.com.ng

Related Posts