Yau, za mu tattauna ne akan yadda ake yin zallar madarar kalaman soyayya da waken soyayya ga masoyiya ko kuma ga saurayi domin a yabe su, ko sanya su cikin nishadi da sanyaya musu ransu.
Wadansu mutanen sun raja’a a kan cewa; ita dai waka baiwa ce! Yayin da wadansu kuma suka ce; a’a ko akwai baiwa a cikin waka to akwai sa kai da naci.
Kuma masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce, naci shi ne maita.
Menene Ma’anar Wake
“Wake wani nau’in waka ne mai dauke da tarin hikima da basira wanda ake rubuta shi, a rera shi ga masu sauraro ba tare da kida ba — Ana iya karanta shi waka-waka, ko kuma karabitin karatu—.”
Ba kowanne wake ne ke zama waka ba, amma ana iya juya mafi akasarin wakoki su koma wake.
Mutum kuma zai iya zama marubucin waka da wake a tare, kai zai ma iya zama mai waka da wake din.
Waken Soyayya
“Shi dai waken soyayya shi ne waken da masoyi ke rubutawa masoyiyarsa.”
A cikin waken zai iya zayyana suffofin abar kaunarsa, ya yabe ta, ya koda ta, ko ya yi mata kirari.
Zai kuma iya cika waken nasa da tsantsar tsagwaron kalaman soyayya masu narkar da zuciyar mai karatu.
Yin waken soyayya ga masoyiya na matukar bukatar yawan yin karatu game da soyayya, musamman litattafan soyayya domin wasu lokutan a ciki ake zakulo wadansu kalaman da ake cakudawa wurin samar da sabon wake.
Misalan Waken Soyayya
Yanzu, zan yi rubutu mai dauke da misalin madarar waken soyayya. A ciki zan saka kalmomi masu tayar da tsohuwar tsumammiyar soyayya.
Title: Ke Daya
“Duniya cike take da jinsi biyu (Rijilu da Nisa’u) amma ni ke kadai na gani a cikin mata.”
“Na zaga gabas da yamma, na bi ta kudu da Arewa, na kurdada, na kewaya amma ban ga kamarki ba, ina ma ki zama matata.”
“Ke daya tilo kadai na gani, tsantsar tsananin ciwon sanki ya gauraye zuciyata.”
“Wayyo masoyiyata, shaukin sonki kadai cire mini damuwar da ke cikin raina yake yi.”
“Ina ma ki zama matata, da ko na sanya kwado na rufe makullin zuciyata na jefa a teku.”
A kula: yana da kyau kowa ya rubuta nau’in wakensa yadda yake so, domin ka’idojin da ke cikin wake karantarsu sai an samu malaman Hausa.
Kalaman Soyayya
Suna daga cikin abubuwa masu saukin furtawa ga mace ko namijin da ku ke so da kauna. Lokuta da dama ana iya koyon nau’ika masu tarin yawa na kalaman soyayya ta hanyar kallon finafinan soyayya ko kuma karanta litattafan soyayya.
Masoyan da su ka yi kaura wurin neman kalaman soyayya masu ratsa zuciya su kan sayi litattafan soyayya domin koyon soyewa da baki.
Duk wata kalma da ka sani, ba za ta wuce ina sonki ba. Ina kaunarki.
Amma in har tafiya ta yi tafiya, akwai lokacin da mace ko namiji za su bukaci iya zafafan kalamai masu ratsa zuciya da sanya ta cikin nishadi da annashuwa.
Misalan Kalaman Soyayya (Maza)
- Ke ce muradin raina, tauraruwar dake haskake zuciyata. Ba na jin zan juri dogon lokaci ba tare da na ji muryarki ko na kalli hotonki ba ko kuma na ganki a zahiri.
- Hakika duk matan duniya ya zame musu wajibi su sallama miki domin tsabagen irin haduwar da ki ka yi.
- Ke kadai ce tawa, ba ni da kowa a raina bayan ke, kullum da kaunaki nake kwana
- Babban burina shi ne na mallakeki a matsayin matata, domin ko ta ina kin hadu, mu’amalarki, kamalarki, sanin ya kamatanki, lallai zan so Allah ya mallaka min ke.
Irin wadannan kalamai na yabo da kambamawa su ya kamata duk wani namiji wanda ke da budurwa ya yi mata musamman yayin da su ke hirar soyayya ta waya.
In kuma gashi ga ita ne, abin ma zai fi dadin fada, amma dai son samu a takaita tashin murya, a kai zuciya nesa a yi wa abar kauna murya tattausa kuma mai dadi.
Misalan Kalaman Soyayya (Mata)
Magana ta fisabilillahi, babu wadanda su ka kai mata yawan karance-karancen litattafan soyayya kai har ma da rubuce-rubucensu. Wannan ya sa iya tsantsara tsara kalaman soyayya masu tausasa zuciya ba za su taba yi musu wahala ba.
Ga dai wasu kalamai domin ku kara a cikin kamus din kalmominku:
- Habibi ka san babu wanda na ke so, na ke kauna fiye da kai. In da za a hade duk mazajen duniya wuri guda, a ce na zaba, to kai zan zaba.
- Murmushinka na sanya ni nishadi, fara’arka na kwantar min da hankali, kalamanka na tausasa raina, gaskiya ba na tunanin zan iya rayuwa ba tare da kai ba.
Gaskiya ba zan iya yinsu duka ba, amma dai ga samfur nan gareku mata. Sai ku dage wurin sace wa da kuma kankame zuciyoyin samarinku gam-gam.
Kammalawa
A nan za mu dasa aya a cikin wannan darasi namu na yau. Kada ku manta ku yi sharhi a kasan rubutun nan domin mu cigaba da wallafa bayanai irin wadannan.